in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matasan DRC za su halarci dandalin yara manyan gobe a Burundi
2014-05-29 10:41:23 cri

A dunkule yara 15 da suka fito daga jahohin jamhuriyyar demokaradiyar Congo DRC za su wakilci kasarsu a birnin Bujumbura na kasar Burundi a yayin dandalin yara manyan gobe, wani dandalin shiyya kan matasa domin zaman lafiya da cigaban yankunan babban tafki da za'a bude daga ranar 31 ga watan Mayu, in ji wata sanarwar kungiyar kula da kananan yara ta UNICEF da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kofinta a ranar Laraba.

Dandalin na cikin tsarin aiwatar da yarjejeniyar da ta shafin zaman lafiya, tsaro da dangantaka tare da kasar DRC-Congo da shiyyar da aka sanya wa hannu a ranar 24 ga watan Fabrairun shekarar 2013 bisa la'akari da yake-yake da tashe-tashen hankali da ake fuskanta a kai a kai a yankin babban tafki.

Wannan dandalin na Burundu zai tattara yara fiye da 50 masu shekarun haifuwa 13 zuwa 17 da suka fito daga kasashen da wannan yarjejeniya ta shafa, tare da tawagogin kasashen DRC, Rwanda, Burundi, Uganda, Zambiya da wasu sauran kasashen wannan shiyya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China