Rundunar sojojin ruwan Najeriya ta ba da wata sanarwa a ranar Lahadi cewa, za ta tura sojoji fiye da dubu daya da za su shiga yaki da masu tada kayar baya dake arewa maso gabashin kasar.
A cewar wata sanarwa ta cibiyar tsaron Najeriya, sabbin mambobin rundunar sojojin ruwan Najeriya sun samu horo domin fuskantar sauye sauyen da ka iyar faruwa ta fuskar tsaro da kuma duk wata bazarana. Sojojin ruwan Najeriya na halarta da ba da gudunmuwa kan kokarin yakin da ake yi da masu tada kayar baya domin kiyaye zaman lafiya a dukkan bangarorin da suka shafi kasar Najeriya.
Daga cikin wadanda suka samu horo, 1060 za su je su cike taimakon da wadanda tuni aka tura suka ba da a cikin ayyukan tsaron cikin gida, in ji rundunar sojojin ruwan Najeriya. (Maman Ada)