Ana sa rai magatakardan MDD Ban Ki-moon zai ziyarci Monrovia, babban birnin kasar Liberia a ranar Juma'a domin ziyarar aiki ta kwana daya.
Wata sanarwa daga gwamnatin kasar Liberia ta ce, magatakardan MDD zai jagoranci wata tawaga ta jami'ai goma sha takwas, cikin jami'an, akwai Margaret Chan, darekta janar ta hukumar lafiya ta duniya WHO.
A yayin ziyarar, magatakardan MDD zai gana da shugabar kasar Liberia Madam Ellen Sirleaf da kuma wadansu manyan kusoshin gwamnatin kasar ta Liberia.
Hakazalika tawagar za ta kuma halarci wani taro a dakin babban taro na Liberia tare da kuma tattaunawa da tawagar MDD dake zaune a Liberia.
Kafin ya bar kasar ta Liberia, magatakardan MDD zai kuma ziyarci wata cibiyar kiwon lafiya dake Monrovia inda ake duba lafiyar ma'aikatan kiwon lafiya. (Suwaiba)