in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya amince da tsawaita wa'adin aikin tawagar UNMIL
2014-12-16 09:34:42 cri

Wakilan kwamitin tsaron MDD sun cimma matsaya guda game da kudurin tsawaita wa'adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta UNMIL mai aiki a kasar Laberiya da watanni 9.

A yayin zaman kwamitin na jiya Litinin ne dai aka amince da baiwa tawagar ta UNMIL karin wa'adin, wanda a yanzu zai kammala a ranar 30 ga watan Satumabar badi.

Bisa wannan kuduri, ana fatan tawagar ta UNMIL za ta kara mai da hankali ga batun tallafawa mahukuntan kasar, wajen karfafa harkokin tsaro, ciki hadda horas da jami'an 'yan sandan kasar hanyoyin magance kalubalolin da ka iya fuskantar kasar a wannan fanni.

Kaza lika ana fatan tawagar za ta ci gaba da ba da agajin jin kai, da taimakawa shirin inganta zabuka, da na kare hakkokin bil'adama. Bugu da kari kwamitin tsaron ya jaddada bukatar ci gaba da karfafa shirin yiwa sassan gudanarwa, da na kundin mulkin kasar kwaskwarima, musamman ma fannonin da suka shafi tsaro, da na sulhu, da na inganta zamantakewar al'umma, da kuma yakin da ake yi da yaduwar cutar Ebola.

Kwamitin na tsaro ya kuma yi fatan daukar dukkanin matakan da suka wajaba, domin tsara shirin farfadowar kasar ta Labariya cikin shekaru masu yawa a nan gaba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China