Kungiyar tarayyar tattalin arzikin yammacin Afrika ECOWAS ta ce, za ta tura jami'ai masu sa ido a kan zaben 'yan majalissar dattawa da za'a yi a kasar Liberiya ranar Asabar din nan mai zuwa.
Kadre Desire Ouedraogo, shugaban kungiyar ya sanar da hakan a Abuja, babban birnin tarayyar Nigeriya lokacin tattaunawar shi da ministan harkokin wajen Liberiya Augustine Kpehe Ngafuan, kamar yadda wata sanarwa da Xinhua ta samu a Monrovia, babban birnin kasar ta Liberiya ta yi bayani.
An yi tattaunawar ne a wani bangaren taron shugabannin kasashen da gwamnatocin yankin karo na 46, kuma an yanke shawaran hakan ne bayan da ministan ya yi wa shugaban kungiyar cikakken bayani game da zaben da ke tafe.
Augustine Ngafuan ya yi wa shugaban na ECOWAS bayanin a kan dage dokar dakatar da zaben da babbar kotun kasar ta yi, wadda yanzu ta ba da damar a yi zaben a ranar Asabar 20 ga watan nan da muke ciki. (Fatimah)