Mahalarta babban taron bunkasa hada-hadar fidda hajoji na kasa da kasa ko WEDF, wanda aka kammala a birnin Kigalin kasar Rwanda, sun bayyana Afirka a matsayin nahiyar dake da kasuwa mai armashi a dukkanin fadin duniya.
A jawabin da ta gabatar yayin bikin kammala taron na yini uku, babbar daraktar cibiyar cinikayya ta kasa da kasa ITC Arancha Gonzalez, ta ce, nahiyar Afirka na da makoma mai haske game da harkokin cinikayya da zuba jari.
Gonzalez ta ce, yayin taron na wannan karo, an tattauna game da hanyoyin hadin gwiwa, da takwarorin nahiyar na kudu maso kudu da suka hada da kasashen Sin, da India, da Brazil da kuma Turkiyya, wadanda wakilansu suka halarci taron domin tattaunawa kan harkokin cinikayya a Afirka.
Daraktar ta ICT ta kara da cewa, kasancewar wadannan kasashen a sahun gaba a fannin zuba jari a kasuwannin duniya, ya sanya su kasancewa abokan hulda da suka dace da Afirka.
Gonzalez ta kuma bayyana taron na bana, a matsayin mafi girma da WEDF ta taba shiryawa, wanda ya samu halartar wakilai 1,200 daga kasashe 73. (Saminu)