Babban jami'in MDD a kasar Libya, Bernardino Leon, ya ce, shekaru ukku bayan kawar da tsohuwar gwamnatin kasar daga karagar mulki, har yanzu jama'ar kasar na cikin wani hali na rashin tabbas, ganin cewa, a kulli yaumin fatan da suke da shi na samun makomar rayuwa ta gari, sai kara subuce masu yake yi, a yayin da ake ci gaba da rikici a kasar ta Libya.
A yayin da yake jawabi ga kwamitin tsaro na MDD, Bernardino Leon,wakilin musamman na babban sakataren MDD ya ce, tuni ya gabatar da kira a kan shugabannin Libya da su dauki mataki na gaggawa domin yin sulhu, da zimmar magance tashin hankalin da ake fama da shi.
Bernardino ya jaddada cewar, duk da yake cewar, ana ta nanata kiran a dakatar da gumuzu, har yanzu ba ta canza zani ba domin kasar na cikin wani hali na dar-dar, kuma kamar yadda ya ce, babu yadda za'a yi a samu wanzuwar sulhu a yayin da ake ci gaba da fada da juna.
Wakilin magatakardan MDD a Libya ya kara da cewar, a Benghazi dake gabashin kasar, ana samun sabbin artabu tsakanin dakarun kasar, kuma ya jaddada cewar, tashin hankalin yana iya kawo barazana ga jama'a farar hula dake kusa da inda ake bata kashin.
Bernardino ya ce, a yammacin kasar ta Libya, ana ci gaba da fuskantar barazanar barin wuta wanda ake yi ba kakkautawa a wasu sassa na Tripoli, kuma tuni hakan ya jefa mutane dake kusa da wurin cikin wani yanayi mai hadarin gaske. (Suwaiba)