in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi tir da kisan jami'in MINUSMA a Mali
2014-09-15 09:25:07 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya bayyana matukar bacin ransa, game da kisan wani jami'in tawagar wanzar da zaman lafiya ta MINUSMA a kasar Mali.

Rahotanni sun nuna cewa, jami'in 'dan kasar Canada ya rasa ransa ne sakamakon wani harin da aka kaiwa motar da suke ciki a Aguelhok, dake yankin Kidal a jiya Lahadi. Kaza lika harin ya sabbaba jikkatar wasu jami'an rundunar su 4.

Wannan ne dai hari na biyu da aka kaddamar kan jami'an na MINUSMA a baya bayan nan, inda kafin hakan wani hari a ranar 2 ga wata, ya hallaka wasu jami'an 'yan kasar Chadi su 4, tare da jikkata wasu 15 a dai wannan yanki na Kidal.

Cikin wata sanarwa da ofishin babban magatakardar MDDr ya fitar, ta rawaito Mr. Ban na bayyana cewa, makamantan wadannan hare-haren da ake kaiwa jami'an tawagar wanzar da zaman lafiya a Malin ba za su taba sanyaya gwiwar majalissar, a kokarin da take yi na agazawa al'ummar kasar ba.

Mali dai na ci gaba da fuskantar barazanar tsaro daga dakarun 'yan aware tun bayan juyin mulkin kasar na shekarar 2012, musamman ma daga yankunan kasar inda 'yan adawa ke da matukar tasiri. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China