in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD za ta binciki musabbabin harin da aka kaiwa dakarun wanzar da zaman lafiya a Mali
2014-09-04 10:11:25 cri

Hukumar da ke kawar da nakiyoyin da aka binne a karkashin kasa ta MDD tana binciken musabbabin mummunan harin da aka kaiwa dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD dake Mali, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 4, yayin da wasu suka jikkata.

Kakakin MDD wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Laraba ya ce, hadarin ya faru ne lokacin da motar da ke dauke da ma'aikatan wanzar da lafiyan ta taka wata nakiya a kan hanyarsu ta zuwa garin Aguelhok dake arewacin kasar ta Mali.

A cewar MINUSMA, ma'aikatan wanzar da zaman lafiya da wannan hadari ya rutsa da su 'yan kasar Chadi ne, yayin da shida daga cikinsu suka ji mummunan rauni.

Kakakin MDD ya ruwaito babban sakataren MDD Ban Ki-moon cikin wata sanarwa na cewa, lamarin shi ne hari na baya-bayan nan da aka kai kan ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na MDD da ke yankin Kidal cikin makonni da suka gabata, ciki har da harin da aka kai da makamin roka kan sansanin MINUSMA, da wani harin da aka kai kan motar da ke dauke da dakarun tawagar ta MINUSMA wanda ya raunata ma'aikatan wanzar da zaman lafiya, 'yan kasar Chadi guda 9 a ranar 29 ga watan Agusta, harin da kwamitin tsaro na MDD ya yi allahwadai da shi. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China