An zabi ministar ma'aikatar albarkatun man fetir ta tarayyar Najeriya Diezani Alison-Madueke, a matsayin sabuwar shugabar kungiyar kasashe masu arzikin man fetir ta OPEC.
Diezani Alison-Madueke dai ita ce mace ta farko da za ta jagoranci wannan kungiya. An kuma zabe ta ne yayin taron kungiyar karo na 166 da ke gudana a birnin Vienna na kasar Austria.
Wata sanarwa da aka fitar a birnin Abujan tarayyar Najeriya ta ce, sabuwar shugabar ta OPEC, za ta rike ragamar kungiyar har tsawon watanni 12, za kuma ta maye gurbin tsohon shugaban ta Abdourhman Atahar Al-Ahirish daga kasar Libya.
Baya ga zaben sabon shugaban kungiyar ta OPEC mai mambobi 12, ana kuma fatan tattauna batutuwan da suka kunshi lalubo hanyoyin dakatar da faduwar farashin danyan mai, da kokarin daidaita farashin sa.
Kaza lika ana fatan binciko hanyoyin samar da cikakkiyar riba ga masu hada-hadar danyan man, tare da tabbatar da wadatar sa ga masu bukata. (Saminu)