Ministocin kungiyar kasashen da ke da arzikin man fetur ta duniya OPEC sun amince da ci gaba da samar da yawan man da suke fitarwa jiya Alhamis, duk kuwa da kasancewar faduwar farashin na man fetur.
Wata sanarwa daga OPEC ta ce, farashin man ya fadi kasa warwas, wanda ba'a taba gani ba a cikin shekaru 4 da suka wuce.
Sanarwar ta ce, shawarar da suka yanke na samar da man fetur a kan ganga miliyan 30 a kulli yaumin an yi shi ne saboda muradai na samun daidaito a kasuwar man fetur ta duniya, musamman saboda rugujewar farashin man fetur a duniya.
Matakin da OPEC din ta dauka yana nufin ke nan man fetur kashi 40 bisa dari da take samarwa a duniya za'a ci gaba da hako shi, kamar dai yadda yarjejeniyar kungiyar OPEC din ta tanada tun daga shekarar 2011. (Suwaiba)