Gwamnatin kasar Aljeriya ta ce, watakila za ta dauki matakan tsuke bakin aljihu, sakamakon faduwar farashin mai a kasuwannin duniya.
Firaministan kasar Abdelmalek Sellal wanda ya bayyana hakan ga manema labarai ya ce, Aljeriya ba za ta iya jurewa matsalolin tattalin arziki sakamakon faduwar farashin mai ba, wannan ya sa gwamnatin daukar wasu matakai don dacewa da wannan hali.
Ya kuma ce, gwamnatin za ta rage manyan ayyukan da ta ke gudanarwa kamar gina hanyoyin jiragen kasa na zamani da kudaden da ta ke kashewa amma ban da muhimman ayyuka a bangaren ilimi.
A ranar Talata ne majalisar ministocin kasar karkashin jagorancin shugaban kasar ta yanke shawarar aiwatar da sabbin matakan tsuke bakin aljihun kasar a kasafin kudin kasar, ciki har da dakatar da daukar ma'aikata a shekara ta 2015. (Ibrahim)