in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan sa kai a Libiya sun hallaka sojoji 18
2014-12-26 10:00:20 cri

Mayakan kungiyoyin Dawn da na Ansar al-Sharia dake kasar Libiya, sun hallaka sojojin gwamnatin kasar 18, yayin wani sumame da suka kaiwa wata bataliyar soji dake birnin Sirte a arewacin kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa, mayakan sun kuma cinnawa wata ma'adanar mai wuta a harin na jiya Alhamis.

A makon da ya gabata ma dai sai da mayakan kungiyar ta Libiya Dawn, suka kaddamar da wani harin na daban, domin abin da suka kira yunkurin 'yantar da filayen haka, da na tara man kasar dake daura da bakin tekun arewacin kasar, yankin da ke tsakanin birnin Benghazi da Sirte.

Mayakan sun kai simamen na makon jiya ne a ma'ajiyar mai dake Sidra, da ta Ras-Lanuf da kuma wadda ke Brega. Yankin dake kunshe da ma'ajiyar mai mafi girma a kasar.

Kungiyar Libya Dawn, na ikirarin cewa, tsohuwar majalissar kasar ta GNC ce ta amince da kafuwar ta.

Dauki ba dadin dake wakana tsakanin dakarun gwamnatocin kasar biyu, ya haifar da raguwar danyan man da ake hakowa a kasar, daga ganga 800,000 zuwa ganga 200,000 tun daga tsakiyar watan nan na Disamba, matakin da ya janyowa Libiyan asarar miliyoyin daloli, tare da illata kasafin kudin kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China