Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir a ranar Lahadin nan ya yi suka ga ayyukan UNAMID a Darfur, yana mai cewa, sun zama wani karin nauyi ga harkokin tsaro.
Ya ce, ayyukun majalissar karkashin UNAMID wani karin nauyi ne ga harkokin tsaro, kuma ga yadda lamuran suke tafiya sun koma ba da kariya ga 'yan tawaye maimakon al'ummar kasar.
Tun da farko dai Sudan ta sanar da cewar, tana son tawagar ta fara shirin ficewa daga yankin Darfur wanda ke fuskantar yakin basasa tun shekara ta 2003.
Rahotanni da aka bayyana a watan Nuwamba sun nuna cewar, sojojin rundunar kasar sun ci zarafin mata da 'yan mata sama da 200 a kauyen Tabit. Abin da gwamnatin kasar Sudan ta fito fili ta musanta tare da ba da izini ga jami'an MDD da su gudanar da bincike, amma sai tawagar UNAMID ta ce, ba ta gano wani shaidan da ya tabbatar da hakan ba.
A lokacin taron manema labarai, shugaban kasar na Sudan ya jaddada cewa, ba zai amince da bincike a zagaye na biyu ba da tawagar majalissar ke shirin gudanarwa. (Fatimah)