in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta saki wasu fasinjojin jirgin sama dake tsare a kasar
2014-12-17 09:52:53 cri

Mahukuntan kasar Libya sun bayyana sakin wasu mutane dake cikin wani jirgin sama su 4, wadanda aka tsare a kasar tun ranar 14 ga watan Nuwamba, bisa zargin keta sararin saman kasar ba tare da neman izini ba.

Rahotanni na cewa, jirgin na dauke ne da mutane 7, ya kuma kutsa sararin saman Libyan daga hadaddiyar daular Larabawa dauke da kayayyakin jin kai wadanda za a kai kudancin kasar.

A cewar ministan harkokin wajen kasar, tsagin masu ra'ayin Islama Mohamed Al-Ghirani, an saki mutane 4 cikin fasinjojin jirgin su 7 ne bisa umarnin babban mai shari'ar kasar, yayin da sauran ukun ke ci gaba da fuskantar tuhuma.

Kawo yanzu dai kasar Libya na fama da sa-in-sa daga bangarori biyu, wadanda kowanensu ke da'awar iko da kasar. Ana kuma danganta matsalolin siyasar kasar da faduwar gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi a shekarar 2011 da ta gabata. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China