Aka kashe a kalla mutane goma sha daya, kana wasu 59 suka jikkata a ranar Litinin a yayin wani kazamin fada tsakanin sojojin gwamnatin masu biyayya ga tsohon janar Khalifa Haftar da masu kishin islama a birnin Benghazi, dake gabashin kasar Libya, a cewar wasu majiyoyin kiwon lafiya da na tsaro.
Majiyoyin kiwon lafiya sun bayyana cewa, wadanda aka kashe yawancinsu sojoji ne da mayakan sa kai dake goyon bayan dakarun Khalifa Haftar. Kungiyon kishin islama ba su bayyana mutuwa ko jikkata daga wajensu ba. Amma kuma ana ganin cewa, mayakan kishin islama za su iyar samun barna sosai daga wajensu. (Maman Ada)