Kwamitin tsaron MDD ya ja hankalin daukacin sassan masu ruwa da tsaki a rikicin kasar Sudan ta Kudu, da su hada gwiwa wajen shawo kan matsalar siyasar kasar, domin kaiwa ga wanzuwar yanayin zaman lafiya da lumana.
Cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a jiya Litinin, wakilansa sun yi amfani da wannan lokaci na zagayowar samun 'yancin kasar ta Sudan ta Kudu, domin nuna takaici na irin yadda ake keta hakkokin bil'adama a kasar, matakin da ya kai ga kisan dubban fararen hula, tare da tilasawa kusan mutane miliyan 2 kauracewa gidajensu a cikin shekara daya tak.
Har wa yau sanarwar ta nuna damuwa ga kisan jami'an MDD masu ba da tallafin jin kai a kasar. Lamarin da aka alakanta da rashin managarcin tsarin jagoranci, da kuma rashin aiwatar da sahihin shirin wanzar da zaman lafiya mai dorewa.
Baya ga haka, sanarwar ta nuna damuwa matuka, game da bijirewa aiwatar da 'yarjejeniyar dakatar da bude wuta da sulhu, wadda aka rattabawa hannu tun a watan Janairun wannan shekara, da ma ta watan Mayun da ya gabata. (Saminu)