in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aljeriya na daukar matakan kare kan iyakokinta daga farmakin 'yan ta'adda
2014-12-22 09:20:44 cri

Wata majiyar tsaro a kasar Aljeriya na cewa, sama da dakarun kasar 4,000 ne suka kaddamar da wani samame na musamman ranar Lahadi a kan iyakar kasar da kasashen Libya da Nijar da nufin fatattakar kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da ke sintirin a kan iyakar.

Manufar shirin wanda kwamandan sojan kasar ya ba da umarnin aiwatar, ita ce kare kan iyakokin kasar, sakamakon rahotannin da mahukuntan kasar suka samu game da shirin da mayaka masu tsattasauran ra'ayi da masu fatauncin makamai ke yi na shiga kasar.

Karuwar barazanar tsaro a yankin Sahel da kasashen da ke makwabtaka da ita, sun tilastawa kasar ta Aljeriya tura karin dakaru kan iyakarta da kasashen Libiya, Tunusia, Nijar, Mali, Mauritaniya da Morocco, don ganin ta dakushe duk wani yunkurin na hare-haren kungiyoyin da ke dauke da makamai da aikata miyagun laifuffuka, ciki har da masu fataucin makamai da miyagun kwayoyi. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China