Sojojin kasar Aljeriya sun kashe shugaban 'yan ta'addan dake da hannu wajen sace da kuma fille kan 'dan kasar Faransa Herve Gourdel a kasar Aljeriya, a cikin daren Litinin, a cewar kafofin watsa labaran kasar a ranar Talata. Da suke ambato majiyoyin tsaro masu tushe, gidan talabijin mai zaman kansa Ennahar TV ya bayyana cewa, Abdelmalek El Gouri, shugaban kungiyar Jund Al-Khalifah dake ikirarin marawa kungiyar IS, an kashe shi a garin Isser mai tazarar kilomita 60 daga gabashin birnin Alger. (Maman Ada)