Kwamitin sulhu na MDD ya dauki niyya a ranar Laraba wajen sake ba da iznin shekara guda ga kasashe mambobi da kuma kungiyoyin shiyya shiyya dake yin hadin gwiwa tare da hukumomin kasar Somaliya wajen yaki da 'yan fashin teku, da kuma sace sace da makamai a cikin ruwan tekun wannan kasa dake kusurwar Afrika.
Kasashe mambobi goma sha biyar na kwamitin tsaro sun bayyana a cikin wani kuduri cewa, sake ba da iznin ya dace da aya ta 7 ta kundin kasa da kasa na MDD, wato ba da iznin yin amfani da karfin soja, da ya shafi wannan aiki kan matsalar guda kawai ta kasar Somaliya, kafin su jaddada cewa, wannan kuduri ya kasance a matsayin wata bukatar kasa da kasa domin warware wannan matsala. (Maman Ada)