Rundunar sojin Najeriya ta ce, ta cafke wasu da ake zargin masu daukar hotuna da nadar faifan bidiyon kungiyar Boko Haram ne.
A cewar kakakin rundunar sojin kasar manjo Janar Chris Olukolade, an kame mutanen wadanda ke nadar yadda 'yan kungiyar ke farwa fararen hula ne yayin wani sintiri na kakkabe yankunan jihar Adamawa daga ayyukan 'yan kungiyar.
Olukolade ya ce, an kame 4 daga cikin su lokacin da suke kokarin tserewa cikin wata mota kirar jeep, dauke da wasu makamai da kuma kyamarori na zamani.
Kungiyar ta Boko Haram dai na ci gaba da zamewa Najeriyar babbar barazana a fannin tsaro tun daga shekarar 2009, lokacin da mayakanta suka fara kaddamar da hare-hare kan fararen hula. A kuma watanni uku da suka gabata kadai, dakarunta sun hallaka daruruwan jama'a, yayin farmakin da suka kai sassa, da kauyukan jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe dake arewa maso gabashin kasar.
Mahukunta a Najeriyar dai na ci gaba da daukar matakan dakile ayyukan wannan kungiya mai da'awar kokarin kafa daular musulunci, wadda ayyukanta suka sabbaba kisan dubban jama'a a cikin wannan shekara ta 2014. (Saminu)