Ministan samar da gidajen kwana na kasar Algeria Abdelmadjid Teboune ya bayyana jiya Lahadi cewar, kasarsa ta ware kudade daga cikin kasafin kudi na kasar har dalar Amurka biliyan 63 domin magance matsalar karancin gidaje da ta addabi kasar nan da zuwa shekarar 2019.
Ministan wanda ya bayyana hakan a yayin ganawa da wadansu jami'ai na gwamnati a yankin Constantine, kilomita 400 daga babban birnin kasar Algiers, ya kara da cewar, kawo ya zuwa yanzu kasar ta ware wadannan kudade tun daga shekarar 2012 har zuwa shekara ta 2019 domin magance wannan matsala.
Teboune ya ba da tabbacin cewar, faduwar farashin man fetur a duniya ba za ta shafi ayyukan samar da gidajen da aka sanya su a cikin shirin raya kasa na shekara ta 2015 zuwa 2019 ba. (Suwaiba)