Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya kori mataimakiyarsa Joice Mujuru da wasu ministocinsa bakwai, a cewar sakataren gwamnatin kasar a cikin wata sanarwa.
A cewar wannan sanarwa, Mugabe ya yi amfani da ikonsa domin tunbuke madam Joice Mujuru daga mukaminta na mataimakiyar shugaban kasa, kujerar da ta rike a tsawon shekaru goma, bisa dalilin cewa, aikinta ya sabawa yadda take tafiyar da aikinta da kuma sakamakon da aka jira kanta, da kuma matsalar hada aikinta da moriyar kanta, a cewar wannan sanarwa. (Maman Ada)