MDD ta bayyana cewar, wani shiri da aka bullo da shi, na samar da tsaro a makarantun Najeriya ya samu gagarumar gudumuwar kudi a daidai lokacin da aka shiga rana ta 50 da aka sace yaran makaranta 'yan mata, fiye da 200 na Najeriya.
Wakili na musamman na babban sakataren MDD a kan ilmi na duniya Gordon Brown, ya bayyana cewar, shirin na samar da tsaro a Najeriya ya samu gudumuwar kudi, har dalar Amurka miliyan 23 a karon farko, domin tabbatar da cewar, makarantu, musamman a arewacin kasar ta Afrika ta yamma, sun sami matakai na tsaro na kare su daga farmaki, sannan kuma za'a dauki matakai na inganta tsaro a makarantun 'yan mata da samari kamar dai yadda kakakin MDD Stephane Dujarric ya bayyana.
A watan Aprilu ne, kungiyar nan mai tsatsauran ra'ayi ta Boko Haram ta sace yara 'yan mata 270 daga makarantarsu, wacce ke garin Chibok.
A arewa maso gabashin Najeriya, kungiyar ta Boko Haram, wacce ta dauki alhakin sace 'yan matan a cikin wani sako na bidiyo, ta yi barazanar sayar da yaran. Sace yaran ya janyo allah wadai daga kasashen duniya. (Suwaiba)