in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta kara tura jami'an tsaro a babban birnin kasar a hali na dar dar
2014-05-05 10:21:06 cri

Hukumomin rundunar 'yan sandan Najeriya, sun bayar da umurnin tura jami'an 'yan sanda masu dimbin yawa a zagayen babban birnin kasar Abuja, domin tunkarar dandalin tattalin arzikin duniya a kan Afrika, wanda za'a yi a ranar 7 ga watan Mayu.

Sipeto janar na rundunar sojin Najeriya, Mohammed Abubakar, ya ce, jibge jami'an tsaron a Abuja ya yi daidai da umurnin fadar shugaban kasar Najeria, da kuma muradin da kasar take da shi na daukar nauyin bakuncin taron cikin kwanciyar hankali da lumana.

Shugaban jami'an 'yan sandan na Najeriya ya baiwa kwamandojin 'yan sanda umurnin daukar mataki na tsauraran matakan tsaro a muhimman wurare da wuraren dake da raunin tsaro, gami da karfafa tsaro a filayen jiragen sama da manyan hanyoyi da kuma hanyoyin birnin da otel-otel da wuraren gudanar da manyan taruka. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China