Tawagar MDD a Libiya ta ja hankalin sassan dake hamayya da juna, da su amince da shirin komawa teburin shawarwari, domin lalubo hanyar kawo karshen tashe-tashen hankula a kasar.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, tawagar ta bukaci daukacin sassan masu ruwa da tsaki a rikicin kasar, da su shiga tattaunawar da ake fatan komawa a ranar Talatar nan.
Ko da yake sanarwar dai ta ce, abu ne mawuyaci, wannan mataki ya kai ga warware rikicin siyasar kasar, a hannu guda akwai fatan hakan zai ba da damar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, da janyewar dakaru masu dauke da makamai daga sassa daban daban na kasar.
Libiya ta fada mawuyacin halin rigingimu ne dai tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Muammar Gaddafi a shekarar 2011. Inda a yanzu haka bangarori biyu dake adawa ke ci gaba da kokawar amshe ikon kasar.
Bisa shirin mika mulki ga zababbiyar gwamnatin kasar, a watan Yunin da ya shude, aka zabi sabbin wakilan majalissar dokokin kasar, wadanda suka maye gurbin tsohuwar babbar majalissar gudanarwar kasar ko GNC a takaice. Sai dai hakan ya hadu da cikas, tun bayan da gamayyar kungiyar 'yan kishin Islama ta "Libya Dawn", ta ki amincewa da hakan, tare da ci gaba da goyon bayan majalissar ta GNC.
Wannan mataki dai ya haifar da kazamin fada tsakanin sojojin kasar da mayakan 'yan kishin Islama a biranen Tripoli, da Zuwarah, da Zawiya, da Sorman da kuma Gharyan. Yayin da kawo wannan lokaci fada ke kara kazanta a birnin Benghazi. (Saminu)