Tawagar ba da tallafi ta MDD dake Libya (UNSMIL) ta sanar cewa, wani sabon zagayen taron kasa zai gudana a ranar Talata mai zuwa domin karfafa zaman lafiya a cikin wannan kasa dake fama da yakin basasa, a cewar wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba.
A cikin sanarwar, UNSMIL ta bayyana cewa, ta tattauna tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa domin yunkurin bullo da hanyoyin da za su taimaka wajen kawo karshen rikicin siyasa da na tsaro a kasar Libya ta hanyar yin shawarwari. Bayan tuntubar juna tare da bangarorin Libya, tawagar UNSMIL za ta kira wani sabon zagayen taron tattaunawar siyasa da zai gudana a ranar tara ga watan Disamban shekarar 2014.
Kasar Libya na fama da rikicin siyasa tun bayan tashe-tashen hankalin shekarar 2011 da suka kai ga kifar da tsohon shugaban kasar Mouammar Gadhafi. (Maman Ada)