Rahotannin daga birnin Anbar dake yammacin Iraqi na tabbatar da cewa, 'yan kungiyar IS wato kasar musulunci sun hallaka 'yan kabilar wannan gari su 67 a ranar Lahadin nan a cikin wani yikin da suke na kisan kabilun dake bin darikar Sunni a cikin 'yan kwanakin nan, kamar yadda mahukuntar tsaron yankin suka tabbatar.
Wannan al'amari dai ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi 2 ga watan nan lokacin da dakarun kungiyar suka kame magidanta na kabilar Albu Nimer lokacin da suke neman tserewa daga kauyen su na al-Tharthar kusa da birnin al-Baghdadi mai tazaran kilomita 200 daga arewa maso yammacin birnin Bagadaza, in ji wata majiya da ta yi wa Xinhua bayanin cikin sirri.
'Yan kungiya nan take suka hallaka mazaje 67 daga cikin iyalan, suna zarge su da goyon bayan rundunar Sahwa dake yi wa gwamnati aiki, in ji majiyar.
Tun da farko dai 'yan kungiyar ta IS sun hallaka mutane 255 daga wannan kabilar bayan da suka kwashe su daga kauyen su da garuruwan dake gundumar Anbar na yammacin kasar. (Fatimah)