Firaministan kasar Algeria Abdelmalek Sellal ya umarci ma'aikatar tallafawa al'umma da kungiyar bayar da agaji ta Red Crescent ta kasar, da su kai kayan abinci da magunguna ga wadanda yaki ya shafa a yankin kudu maso yammacin kasar Libya da ke makawbtaka da kasar.
Firaministan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, yayin da shi ma wani mamba a kwamitin samar da agaji na yankin Djanet Amer El Koni ya ce, mazauna wadannan yankunan ba su da kungiyoyin agajin da za su tallafa musu fita daga wannan kangi.
Ya ce, gwamnatin Algeria ta yanke shawarar tuntubar shugabannin kabilu da kungiyoyin agaji da ke Libya, ciki har da kungiyar bayar da agaji ta Red Crescent ta Libya domin yin aiki tare, ta yadda za a yi safarar kayan abinci da magunguna ga mutanen da yaki ya shafa a yankunan Ghdames da Ghat.
A ranar Laraba ne kashin farko na kayan agajin ya isa kan iyaka, inda za a tsallaka da shi zuwa Tinalicom tsakanin Algeria da Libya, kafin a samu iznin hukumomi don shigar da shi yankunan Libya.
A watan Mayu ne kasar ta Algeria ta yanke shawarar rufe kan iyakokinta tun bayan da rikici ya rincabe a Libya. Yanzu haka Algeria ta tura dakaru 50,000 kan iyakarta da Libya don hana mayakan al-Qaida shigowa cikin kasar. (Ibrahim)