in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aljeriya ta kori 'yan Nijar fiye da 3000, in ji faraministan Nijar
2014-11-28 10:48:50 cri

Gwamnatin kasar Aljeriya ta dauki matakin korar 'yan Nijar fiye da 3000 dake zaune a cikin kasarta, in ji faraministan kasar Nijar Brigi Rafini a ranar Laraba a gaban 'yan majalisar dokoki a birnin Niamey. Mista Rafini ya ba da wannan labarin a yayin muhawarar matakin tsige da 'yan majalisar jami'iyyar adawa suka ajiye kan gwamnatinsa, dalilin rashin mulki na gari. 'Yan Nijar da wannan matakin ya shafa su ne wadanda suka rasa aikin yi, kana suke bara a kasar Aljeriya, in ji Rafini tare bayyana cewa, yara sun kwashe kashi 70 cikin 100 daga cikin gungun wadannan mutane a yayin da mata suka kai kashi 20 cikin 100.

Kasashen biyu dai sun cimma yarjejeniyar jigilar wadannan bakin haure cikin yanayi mai kyau, in ji faraministan Nijar. Haka kuma kasar Aljeriya ta yi alkawarin tallafawa gwamnatin Nijar wajen samar da sana'ar yi ga wadannan mutane da aka maido kasarsu. A bangaren gwamnatinsa, Rafini ya bayyana cewa, an dauki dukkan matakan da suka dace domin mai da wadannan mutane zuwa kauyukansu na asili. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China