Rahotanni na nuni da cewar, an kashe mutane da dama a yayin da wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka aiwatar da wani hari a garin Bajoga dake jihar Gombe, wacce ke arewa maso gabashin Nigeria.
Mayakan Boko Haram sun kai farmaki a garin na Bajoga a daidai karfe biyar na safiyar Alhamis, jim kadan bayan al'ummar musulmai sun kammala sallar asuba.
Wata majiyar 'yan sanda na nuni da cewar, masu tada kayar bayan sun shiga garin a cikin wasu motoci samfarin Toyota Hilux, da shigar su kuma sai suka farwa mutanen garin da harbi tako-ina, hakan ya sa dole mutane suka tsaya cikin gidajensu, wasu kuma suka ruga daji.
Wani 'dan jaridar kamfanin dillancin labarai na Xinhua dake jihar ya ce, jami'an tsaro sun yi ta dauki ba dadi da 'yan kungiyar ta Boko Haram har tsawon awoyi 3 kafin aka samu nasarar kora su.
Majiyar 'yan sanda ta ce, maharan sun kai farmaki tare da ragargaza babban ofishin 'yan sanda na jihar, da kuma daya daga cikin bankunan garin.
Daga baya 'yan ta'addan sun kama hanyar garin Ashaka dake cikin karamar hukumar Funakaye, inda dama kuma sun taba kai wa garin hari a ranar 30 ga watan Oktoba inda har suka raunata wani 'dan sanda.
Kakakin 'yan sanda na jihar ta Gombe Fwaje Atajiri ya ce, a yanzu kura ta lafa a wuraren da aka kai harin. (Suwaiba)