Kungiyar shuwagabannin kasashen gabashin Afirka ta IGAD, ta fara gudanar da sabon taron masu ruwa da tsaki, game da rikicin kasar Sudan ta Kudu. A baya ma dai wannan kungiya ta sha yunkurin shiga tsakanin bangarorin kasar masu adawa da juna, tun bayan barkewar fadace-fadace tsakanin tsagin gwamnati da na 'yan adawa tsahon shekara guda.
Duk dai da cewa, an cimma matsaya game da batun tsagaita wuta tsakanin bangaren gwamnati da na 'yan adawa, kawo yanzu sassan biyu na ci gaba da fafatawa a kai a kai.
Cikin jawabin da ya gabatar yayin bikin bude shawarwarin na wannan karo, wakilin babban sakataren kungiyar ta IGAD Tewolde Maskal, ya ce, kokarin da kungiyar ta yi a baya, ya haifar da sakamako mai ma'ana, ciki hadda rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta, tare da kira ga shuwagabannin bangarorin biyu, da su rungumi hanyar siyasa wajen warware takaddamar da ke tsakanin su.
Maskal ya kara da cewa, rashin martaba yarjejeniyar tsagaita wutar ya jefa dubban al'ummar Sudan ta Kudu cikin mawuyacin hali.
Kafin bude wannan taro da yanzu haka ke gudana a birnin Adis Ababan kasar Habasha, babban jami'i mai wakiltar manzannin kungiyar ta IGAD Seyoum Mesfin, ya jaddada kira ga al'ummar Sudan ta Kudu, da su kauracewa duk wasu matakai, daka iya kara rura wutar rikicin da ke addabar kasar a yanzu haka. (Saminu)