in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya bukaci a sake tattaunawa tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu
2014-12-12 10:02:59 cri

Kwamitin tsaron MDD ya bukaci bangarorin Sudan da na Sudan ta Kudu, da su gudanar da muhimman shawarwari, domin warware banbance-banbancen dake tsakanin su ta fuskar tsaro.

Wata sanarwa da kwamitin ya fitar a jiya Alhamis, ta yi na'am da ziyarar da shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu ya kai kasar Sudan a ranar 4 ga watan Nuwamba. Yayin wannan ziyara ne kuma shugabannin biyu suka fidda wata hadaddiyar sanarwa, mai kunshe da aniyarsu, ta inganta huldar diplomasiyya, tare da karfafa hadin gwiwar kasashen nasu.

Game da halin da ake ciki a yankunan da kasashen biyu ke takaddama a kansu kuwa, kwamitin na tsaro ya bayyana damuwa don gane da yanayin dar-dar da ake ciki, musamman ma a yankin nan na Abyei mai arzikin mai.

Zaka lika kwamitin tsaron MDDr ya zayyana wasu yankunan kan iyakar kasashen guda 5, a matsayin manyan sassan dake janyo takaddama, wadanda kuma ya kamata a gaggauta warware batu a kansu.

Bugu da kari, kwamitin ya bayyana damuwa game da halin jin kai na kusan shekaru 3, da al'ummun yankunan kudancin Kordofan da na jihar Blue Nile a Sudan suke fuskanta, sakamakon yaduwar tashe-tashen hankula, wadanda suka haifar da gudun hijira, da karancin abinci, da matsalolin tsaro a yankunan.

Tun dai cikin shekarar 2011 ne dakarun kasar ta Sudan suka fara dauki-ba-dadi da mayakan 'yan tawayen SPLM tsagin arewacin kasar, jim kadan da samun 'yancin kan kasar Sudan ta Kudu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China