in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta kara kayayyakin da ba su shafi mai ba da take fitar wa zuwa kasashen ECOWAS
2014-08-29 15:45:39 cri

Ministan masana'antu, ciniki da harkokin zuba jari na Najeriya, Mr. Olusegun Aganga ya bayyana cewa, Najeriya na duba yiyuwar kara kayayyakin da ba su shafi mai ba da take fitar wa zuwa kasashen ECOWAS da darajarsa za ta kai Naira biliyan 116.5 ya zuwa shekara ta 2015.

Ministan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin da yake jawabi a taron majalisar zartaswar masana'antu, cinikayya da harkokin zuba jari na kasa a garin Markurdi, babban birnin jihar Benue.

Bikin na bana ya hallara kwamishinonin masana'ntu, cinikayya da harkokin zuba jari daga jihohin kasar ta Najeriya, inda za su tattauna kan dabarun bunkasa harkokin tattalin azriki ta hanyar ci gaban masana'antu, cinikayya da zuba jari.

Ministan ya ce, ma'aikatarsa ta kammala bullo da wasu dabarun inganta harkokin cinikayya na kasa, wadanda za a sanya su cikin manufofin raya masana'antu, cinikayya da harkokin zuba jarin kasar, a matsayin wani bangare na kokarin kara yawan kayayyakin da ba su shafi mai ba da kasar ke fitar wa.

Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ta himmatu wajen fadada bangaren tattalin arzikin kasar ta hanyar bullo da manufofi da za su bunkasa harkokin cinikayyar cikin gida da waje, tare da janyo hankalin masu sha'awar zuba jari daga ketare, tare da kara irin gudumawar da masana'ntun kasar ke bayar wa na kayayyakin da ake kerawa a cikin gida. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China