A Najeriya wata kotun soji dake zaman ta a birnin Abuja, ta zartas da hukuncin kisa kan wasu sojoji su 54, bayan tabbatar da zargin da aka yi musu na cin amanar kasa.
Bayan sauraron karar da aka gabatar mata, kotun ta ce, ta samu wadanda aka tuhumar da laifuka biyu, masu alaka da hada kai domin aikata laifi, da kuma bijirewa umarnin jagoran su. Sai dai wasu sojojin su 4 sun samu kubuta daga tuhumar, bayan da kotun ta ce ba ta same su da wani laifi ba.
An dai fara gudanar da shari'ar wadannan sojoji ne tun tsakiyar watan Oktobar daga shude, biyowa bayan zargin da aka yi musu na bijirewa jagoran su, da kin amincewa su shiga yakin da rundunar su ke yi da 'yan Boko Haram a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.
Sojojin 54 su ne rukuni na biyu, da aka yankewa hukuncin kisa cikin wannan shekara, sakamakon zargin su da cin amanar kasa. (Saminu)