Gwamnatin Najeriya ta bukaci a ranar Litinin ganin an kafa wata kungiyar hadin gwiwa ta kasa da kasa mafi karfi da kwarewa domin kawar da ta'addanci, matsalar fashin teku da masu kaifin kishin islama a shiyyar yammacin Afrika.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi wannan kira a yayin jawabinsa na bude zaman taron kwamitin shugabanni da gwamnatoci na kungiyar ECOWAS karo na 46 a Abuja, babban birnin kasar.
Ko da yake shiyyar yammacin Afrika ta samu nasarori ta fuskar demokaridiya da bunkasuwar tattalin arziki, amma har yanzu tana fuskantar wasu matsalolin tsaro da na kiwon lafiya, musamman ma dalilin annobar cutar Ebola.
Shugaba Jonathan ya jaddada cewa, matsalolin suna da munanan tasiri kai tsaye wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da ci gaban shiyyar. Babban abin dake tada hankali sosai shi ne bala'in ta'addanci da yanzu ke kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron shiyyar, in ji mista Jonathan. Shugaban Najeriya ya jaddada wa mahalarta taron niyyar Najeriya ta tashi tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar yammacin Afrika. (Maman Ada)