Gwamnatin kasar Nijar ta tura wata tawaga domin halartar wani zaman taro tun ranar Litinin a birnin Geneva tare da kungiyoyin ba da lamuni na duniya, da zummar tattara ragowar kudaden da za su shiga wajen gina madatsar ruwan Kandadji, tun bayan da hukumomin kasar ta Nijar suka karbe kwangilar wannan aiki daga kamfanin Zarubezhvodstroy na kasar Rasha a cikin watan Yulin da ya gabata, a cewar wata majiya mai tushe.
Mukasudin wannan ziyara ta Geneva shi ne don ganin kasar Nijar ta samu ragowar kudaden wannan aiki da suka tashi zuwa kusan dalar Amurka miliyan 176 daga aminan arzikinta
Babban burin gwamnatin kasar Nijar shi ne sake ingiza wannan aiki a cikin watan Febrairu mai zuwa, tare da fara dukkan wasu ayyukan da suka jibanci gina madatsar ruwan Kandadji.
Tun bayan da gwamnatin Nijar ta gano kasawa daga kamfanin kasar Rasha wajen gina madatsar ruwan Kandadji wadda ke da babban muhimmanci ga al'ummar kasar Nijar baki daya bisa lokacin da aka tsai da, hukumomin kasar sun yanke shawarar soke wannan kwangila ba tare da wani jinkiri ba. (Maman Ada)