Kwamitin tsaro na MDD ya kara wa'adin takunkumin hana jigilar makamai zuwa watanni goma kan kasar Liberiya da har yanzu matsalar ke kasancewa barazana ga zaman lafiya da tsaro a shiyyar.
Wannan takunkumin da MDD ta kakabawa Liberiya tun daga shekarar 2003, an aiwatar da shi bisa kuduri mai lamba 1521 na kwamitin sulhu. An kuma cimma wannan sabon kuduri mai lamba 2188 a ranar Talata bisa babban rinjaye na mambobin kwamitin goma sha biyar, ta hakan ne kwamitin ya dauki niyyar kara mikawa gungun kwararru kan Liberiya nauyin kulawa girmama aiwatar da takunkumin kan makamai, da wasu sabbin ayyukan da zai yi tare da hadin gwiwar gwamnatin Liberiya da kuma gungun kwararru kan kasar Cote d'Ivoire. Haka kuma tawagar kwararrun za ta kai ziyarar aiki a kasar Liberiya da kasashen makwabtanta domin gudanar da bincike kan batun. (Maman Ada)