Gwamnatin kasar Liberiya ta sanar a kwanan nan cewa, ta sanya hannu kan mutanen nan goma sha bakwai da ake zargin suna dauke da cutar Ebola da suka gudu a makon da ya gabata a wata cibiyar tsugunar da maras lafiya dake unguwar West Point dake tsakiyar birnin Monrovia.
Ministan watsa labaran kasar Lewis Brown ya bayyana hakan a yayin wani taron menama labarai a Monrovia cewa, maras lafiya dake zargin suna dauke da cutar Ebola, an isar da su zuwa wata sabuwar cibiyar kula da cutar Ebola da aka kafa a asibitin John F. Kennedy dake Monrovia.
Wadannan mutane goma sha bakwai na daga cikin gungun mutanen da ake zargin suna dauke da cutar Ebola 37 da aka tilastawa gudu daga cibiyar West Point yayin da matasan wannan unguwa dake adawa da kafa cibiyar a wurinsu. (Maman Ada)