in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya kara wa'adin tawagar MINUL a Liberiya
2014-09-16 10:28:43 cri

Kwamitin tsaro na MDD ya amince a ranar Litinin ga kara wa'adin tawagar MINUL a Liberiya har zuwa ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2014 bisa la'akari da cewa, halin da ake ciki a wannan kasa na ci gaba da kawo barazana ga zaman lafiya da zaman karko na shiyyar.

A cikin wani kudurin da aka cimma a ranar Litinin, mambobin kwamitin tsaro sun nuna damuwarsu sosai game da annobar cutar Ebola dake ci gaba da kasancewa babban bala'i a cikin wannan kasa, har zuwa kasashen Guinea da Saliyo.

Bisa wannan, mambobin kwamitin sun yi maraba da kaddamar da shirin aiki kan Liberiya domin gaggauta yaki da cutar, kana kuma sun amince da ayyukan jami'an tsaron kasar suke yi, musammun ma a bangarorin wayar da kan jama'a, da kuma wajen yin rigakafi.

Kwamitin ya nuna yabo kan karfafa dangantaka shiyyar domin fuskantar wannan barazana, tare da taimakon kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) da kungiyar tarayyar Afrika (AU) domin dakatar da yaduwar cutar Ebola. Kwamitin tsaro ya bukaci gamayyar kasa da kasa da ta ba da amsa cikin gaggawa kan karancin jami'an kiwon lafiya da suka kware, da kayayyakin da suka dace, in ji kudurin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China