in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taliban a Pakistan ta nada Asmatullah Shaheen a matsayin shugabanta na rikon kwarya
2013-11-04 10:22:10 cri

A ranar Lahadin nan 3 ga wata, kungiyar Taliban ta kasar Pakistan ta sanar da nada Asmatullah Shaheen a matsayin shugabanta na rikon kwarya bayan da aka samu bambancin ra'ayi wajen zaben shugaban da zai maye gurbin tsohon shugaban ta Hakimullah Mehsud da aka hallaka lokacin wani harin da Amurka ta kai na jirgin da ba ya da matuki a ranar Jumma'ar nan da ta gabata, in ji gidajen yada labaran kasar da suka alakanta bayanin daga bakin wani wanda ba'a bayyana sunansa ba.

Rahotannin farko sun nuna cewa, an zabi Khan Syed da aka fi kira Khalid Saina a matsayin sabon shugaba, amma kakakin kungiyar na yankin kudancin Waziristan ya musanta zaben, yana mai cewa, za'a zabi shugaban nan da wassu kwanaki masu zuwa.

Asmatullah Shaheen da aka fi sani da Asmatullah Bhittani, shugaban kungiyar ne reshen arewa maso yammacin yankin kabilar dake kudancin Waziristan kuma zai jagoranci tafiyar da harkokin kungiyar na yau da kullum, in ji sanarwa da kungiyar ta bayar.

Ministan harkokin cikin gida na Pakistan Nisar Ali Khan a ranar Asabar ya yi tir da wannan harin da Amurka ta kai, wanda ya yi sanadiyar kisan Hakimullah, yana mai cewa, wannan ya sa kasar za ta sake nazarin dangantakarta da Amurka domin harin wani shiri ne na lalata kokarin da Pakistan din ke yi na samar da zaman lafiya.

Ministan ya kuma sanar cewa, gwamnati ta dakatar da ziyarar da wassu mambobin zuwa arewacin Waziristan inda aka shirya wani zama na tattauna zaman lafiya tsakaninta da kungiyar ta Taliban.

Haka kuma ma'aikatar harkokin wajen kasar ta yi sammacin jakadan kasar Amurka dake Islamabad Richard Olson, inda ta mika mashi korafinta game da wannan harin da Amurka ta kai, tana mai jaddada cewar, harin da ake kaiwa na jirgin da ba ya da matuki wani aiki ne da ya saba wa dokar 'yancin kasar Pakistan da kuma ikon dokokin duniya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China