in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mullah Fazalullah ya zama sabon jagoran Taliban a Pakistan
2013-11-08 09:53:50 cri

Rahotanni daga Pakistan na cewa, kungiyar 'yan kaifin kishin islaman nan ta Taliban, ta nada Mullah Fazalullah a matsayin sabon jagoranta, kwanaki shida bayan wani harin jirgin sama maras matuki na Amurka, ya hallaka tsohon shugaban kungiyar Hakimullah Mehsud.

Kakakin kungiyar Shahidullah Shahid ne ya tabbatarwa manema labarai hakan ta wayar tarho a ranar Alhamis 7 ga watan nan. Fazalullah ya ce, manyan kwamandojin kungiyar ne suka yanke shawarar nadin Fazalullah, bayan wata ganawar sirri da suka gudanar a wani boyayyen wuri dake arewacin Waziristan.

Fazalullah, wanda a cikin shekarun 2008 zuwa 2009 ya jagoranci wasu hare-hare da 'ya'yan kungiyar suka kai a arewa maso yammacin Swat Valley, ya tsere daga Pakistan zuwa kasar Afghanistan. Jami'an tsaron kasar ta Pakistan sun ce, wannan kwamanda na Taliban ya ci gaba da shirya hare-hare kan dakarun gwamnatin kasar, musamman wadanda ke yankunan kan iyakar kasashen biyu, daga maboyarsa dake lardin Nuristan.

Masu fashin baki dai na ganin nadin Fazalullah na iya sake dagula batun tattaunawar da mahukuntan Pakistan din ke fatan ci gaba da gudanarwa da kungiyar ta Taliban, kasancewarsa daya daga wadanda ake ganin na da matukar tsattsauran ra'ayi. Har ila yau a baya mahukuntan kasar sun sha yin kira ga gwamnatin Afghanistan, da ta mika Fazalullah gida domin fuskantar shari'a, ko da yake gwamnatin Afghanistan din ba ta taba ayyana kasancewarsa a wancan yanki na Nuristan ba.

Tuni dai gwamnatin Pakistan ta soki harin jirgin sama maras matuki da Amurka ta kaddamar a ranar Juma'ar da ta gabata, wanda ya hallaka Hakimullah Mehsud, tana mai cewa, harin ya haddasa babban koma baya, ga shirin wanzar da zaman lafiya da take kokarin yi da kungiyar ta Taliban. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China