Kasar Sin ta ga saurin da masana'antu a bangaren fasahar zamani suka samu tsakanin shekarar 2008 zuwa 2013, wata alama dake nuna kwaskwarima a tattalin arziki, in ji wani jami'in kasar.
Jami'in ya ce, akwai manyan masana'antun kimiyyar fasaha 26,894 ya zuwa karshen shekarar 2013, abin da ya kai kashi 7,8 a cikin 100 na daukacin manyan masana'antun kasar wanda ya karu da kashi 1.3 a cikin 100 bisa ga na shekarar 2008.
Don haka masana'antun sun samu ribar kudin zunzurutu har yuan biliyan 723.37 kwatankwacin dallar Amurka biliyan 118.23 a shekara ta 2013, wato ya karu da kashi 165.5 a cikin 100 idan aka kwatanta da na shekara ta 2008, bisa sakamakon kididdigar tattalin arzkin karo na uku da ma'aikatar kididdiga ta kasar ta fitar.
Wannan karuwan ribar yana kan kashi 11.5 fiye da adadin matsakaitan masana'antu. (Fatimah)