in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakiliyar musamman ta MDD ta yi kiran samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu
2014-10-23 10:35:16 cri

Shugaban ofishin MDD a Sudan ta Kudu, kuma wakiliyar magatakardan MDD ta musamman a Sudan ta Kudu, Ellen Loj, ta yi kira a Laraba a kan kasashen duniya da su taimaka wajen zaburar da tattaunawar sulhu tsakanin kungiyoyi masu yakar juna a Sudan ta Kudu domin kamar yadda ta ce, lokaci ya yi da za'a dakatar da wahalhalun da jama'a ke fuskanta a kasar.

A yayin bude wani taro na kwamitin tsaro na MDD, Loj ta ce, dole ne a kawo karshen yaki da bindigogi, tare da daukar mataki nan take na shimfida cikakkiyar yarjejeniyar samar da zaman lafiya domin mai da kasar a kan turbar zaman lumana na din-din-din.

Wakiliyar magatakardan MDD ta ci gaba da cewar, bayan ta yi sati 6 a Sudan ta Kudu, hakan ya sa ta kara amanna a bisa cewar, rashin yarjejeniya a siyasance na taimakawa wajen kara tabarbarewar al'amurra a Sudan ta Kudu.

Wakiliyar ta yi kira a kan kwamitin tsaron MDD da shugabannnin yankuna da kuma abokanan Sudan ta Kudu da su ci gaba da tuntubar kungiyoyi masu fada da juna domin zaburar da tsarin samar da zaman lafiya mai dorewa.

A halin da ake ciki, kusan mutane kimanin dubu 100 ne suka rasa muhallansu a sakamakon yakin na Sudan ta Kudu, kuma yawancinsu suna zama ne a cibiyoyin MDD na kasar ta Sudan ta Kudu, ta kara da cewar, sojojin kiyaye zaman lafiya na ci gaba da samar da kariya ga farar hula da sauran jama'a marasa galihu. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China