Mataimakin magatakardan gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a Liberia Herve Ladsous ya ce, kawo ya zuwa yanzu, lamarin tsaron Liberia bai shiga cikin wata matsala ba, ta samu koma baya sakamakon barkewar cutar Ebola, wacce ta fi kamari a Liberia.
Herve Ladsous, wanda ya gabatar da jawabi a game da ayyukan da MDD ke yi a Liberia a gaban kwamitin tsaro na MDD ya ce, a yanzu babu sauran wasu alamu dake nuni da cewar, halin tsaro zai tabarbare a kasar ta Liberia a daidai lokacin da yaduwar cutar Ebola ta yi muni a kasar.
To amma Ladsous ya ce, ya kamata a halin da ake ciki, a janye duk wata shawara da aka yanke a game da janye sojojin da 'yan sanda na MDD daga Liberia.
Ya kara da cewar, a yayin da kasashen duniya ke kara kaimi wajen dakile cutar Ebola, ya kamata a hada hannu wajen tunanin samar da goyon baya na kara gina Liberia a karshen matsalar Ebola.
A jiya Laraba, wakilin magatakardan MDD na musamman David Nabarro, shi ma ya gabatar da wani jawabi ga kungiyoyi masu zaman kansu, a inda ya ce, duk da yake akwai alamu na nuna ci gaba wajen dakile cutar ta Ebola, to amma fa ya ce, akwai sauran rina a kaba, saboda babu wani tabbaci a game da yanayin yaduwar cutar ta Ebola mai kisan bil'adama. (Suwaiba)