in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin wanzar da zaman lafiya na kasar Sin sun isa Liberia
2013-10-24 10:22:03 cri

Wani rukunin dake kunshe da jami'an 'yan sandar kwantar da tarzoma 140 na kasar Sin wanda a ciki akwai mata bakwai ya isa kasar Liberia tun ranar Laraba domin gudanar da aikin tabbatar da zaman lafiya bisa kokarin taimakawa aikin MDD, a cewar kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Rukunin wadannan jami'an tsaro na karkashin jagorancin babban kanal 'yan sanda Gai Lixin kuma ya isa wannan kasa ta jirgin sama kirar Boeing 767-200 Utair na musammun da MDD ta yi hayar wajen jigilarsu kuma sun samu tarbo a zuwansu daga jakadan kasar Sin dake Liberia mista Zhao Jianhua da wasu manyan jami'an tsaro dake cikin tawagar MDD game da kasar Liberia (UNMIL).

Sojojin wanzar da zaman lafiya na kasar Sin, za'a tura su zuwa birnin Greenville dake kudu maso gabashin kasar domin ba da taimako wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kuma wa'adin aikin zai kwashe kimanin watanni takwas, in ji jakada Zhao. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China