in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi allahwadai da kara barkewar tashin hankali tsakanin dakarun Sudan ta Kudu da 'yan tawaye
2014-10-31 15:32:49 cri

Magatakardan MDD Ban Ki-moon ya yi suka da kakkausar murya a kan sabunta rikici tsakanin kungiyar sojojin gwamnati da 'yan adawa a jihohin Bentui da Rubkona wadanda ke jihar Unity a Sudan ta Kudu.

Wata sanarwa wacce ta fito daga kakakin magatakardan MDD ta ce, kara fadawa cikin hali na tashin hankali ya sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma kawo cikas ga kokarin da ake yi na kasa da kasa na magance rikicin na Sudan ta Kudu.

Magatakardan MDD ya yi kira a kan shugaban kasar ta Sudan ta Kudu Salva Kiir da Riek Machar da su tsagaita wuta nan take, tare da tabbatar da kariyar farar hula da kuma gine-ginen na MDD. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China