in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Benin ya nuna yabo da nasarorin da UEMOA ta samu a cikin shekaru 20
2014-10-20 10:41:10 cri

Shugaban kasar Benin Boni Yayi ya nuna yabo a ranar Lahadi da nasarorin da kungiyar tattalin arziki da kudi ta yammacin Afrika (UEMOA) ta samu, a jajibirin bikin taya murnar cikon shekaru 20 na kungiyar shiyyar da zai jagoranta a Ouagadougou, babban birnin Burkina-Faso, a matsayin shugabanta a wannan karon.

Ya bayyana cewa, UEMOA ta ci nasarar gina, tsakanin kasashe mambobinta, wani yankin tattalin arziki mai armashi, na hadin gwiwa kuma daga dukkan fannoni. A cikin tsawon shekaru ashirin, a cimma muhimman nasarori domin kyautata jin dadin zaman rayuwar al'ummominmu ta hanyar aiwatar da ayyuka da dama da tsare-tsaren ci gaba, a karkashin shirin tattalin arzikin shiyya, da kusanto tattalin arzikinmu, kasashenmu da al'ummominmu, in ji shugaba Boni. Wadannan su ne, kamar yadda ya bayyana, samar da ruwa a kauyuka, da tsaron abinci da na gina jiki, kiwon lafiya, ilimi, gine-ginen samar da makamashi, hanyoyi, layoyin dogo, tashoshin ruwa da sadarwa.

A cewar mista Boni Yayi, duk da wadannan ci gaban da aka samu, akwai muhimman kalubalolin dake jiran a zare damtse kansu, misalin ayyukan tada muhimman shingayen dake kawo tarnakaki ga cigaban kasashe mambobin kungiyar UEMOA.

Ya kamata mu aiwatar, a cikin hadin gwiwa da taimakon juna, wajen kawo sauye-sauye ga salon tattalin arzikinmu, ta yadda za'a iyar warware cikin karko dukkan kalubalolin dake gaban kasashen mu, musammun ma na zaman lafiya, tsaro da zaman jituwa, tsaron abinci da na gina jiki, da ma batutuwan da suka shafi aikin yi na matasa da mata, a cewar shugaba Boni Yayi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China