Shugaban hukumar zabe ta kasar Tuinisia, Chafik Sarsar ya ce, za'a gudanar da zaben shugaban kasar karo na biyu a ranar 21 ga watan Disambar da muke ciki.
Shugaban ya ce, za'a gudanar da zaben ne zagaye na biyu a tsakanin shugaban kasar na yanzu wanda ke kan karagar mulkin kasar Moncef Marzouki da Beji Caid Essebsi, shugaban jam'iyyar Nidaa Tounes, wadanda su ne a kan gaba da yawan kuri'u a zaben shugaban kasa na farko da aka yi.
Shugaban zaben ya ce, a zaben farko, Essebsi ya zanto kan gaba da kuri'u kashi 39.46 bisa dari a inda kuma shugaban kasar dake kan gadon mulki ya samu kashi 33 .43 bisa dari na kuri'un da aka kada.
A bayan zaben shugaban kasar dake kan gado ya daukaka kara a kotu saboda rashin amincewa da sakamakon zaben shi, kuma kotun ta yi watsi da bukatun shugaban kasar. (Suwaiba)