A jiya Lahadi ne 'yan kasar Tunisia da suka cancanci kada kuri'a suka yi zaben shugaban kasa na farko tun bayan zanga-zangar juyin-juya halin watan Disamban shekarar 2010 da watan Janairun shekarar 2011 a kasar.
Firaministan wucin gadin kasar Beji Caid Essebsi shi ne 'dan takarar jam'iyyar Nidaa Tounes a zaben shugaban kasar, yayin da magoyan jam'iyyar Ennahdha ke marawa Moncef Marzouki baya.
Sai dai bayanai na nuna cewa, mutane kalilan ne suka fito a zaben shugaban kasar na jiya, inda kimamin kashi 70 cikin 100 na wadanda suka cancanci kada kuri'a suka fito.
Kakakin ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Mohamed Ali Aroui, ya bayyana cewa, an girke jami'an tsaro kimamin 100,000 a cibiyoyin kada kuri'a da ke sassa daban-daban na kasar, baya ga dakarun yaki da ta'addanci don ganin zaben ya gudana cikin lumana.
Kakakin jam'iyyar Ennahdha Zied Laadhari ya ce, jam'iyyarsu za ta bude kafar yin hadaka, amma ba su bayyana yadda hadakar za ta kasance ba.
Za a bayyana sakamakon zaben ne cikin 'yan kwanaki, amma idan ba a samu wanda ya lashe adadin da ake bukata, da alamun za a kai ga zagaye na biyu. (Ibrahim)